Monday, September 2, 2019

Yanzu-yanzu: Mutane 3 sun hallaka, yan kasar Afrika ta kudu na kona shagunan yan Najeriya

An hallaka akalla mutane uku yayinda aka kona dukiyoyi a sabon harin da yan kasar Afrika ta kudu suka kai wa yan kasashen ketare dake zaune a kasar musamman yan Najeriya.
A cewar shugaban kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta kudu, Adetola Olubajo, ya ce an fara kai wannan hare-haren ne da safiyar Lahadi, 1 ga watan Satumba a unguwar Jeppestown na garin Johannesburg.
Ya ce fusatattun matasan sun bankawa wani gida wuta a unguwar.
Yace: " Hakazalika sun yi fashi a shagunan da ke unguwar da aka san na yan kasashen ketare ne. Amma daga baya jami'an yan sanda suka fitittikesu kuma suka damke wasu."
"Da yammacin Lahadi kuma, wasu matasan da ake zargin mazaunan Zulu ne suka mamaye unguwar Mailvern a birnin Johannesburg inda sukayi sace-sace kuma suka kona shagunan mutane."
"Lokacin da na samu labarin da yamma, da wuri na sanar da yan sanda a Jeppestown amma an rika an aikata ta'asa mai ban haushi."Olubajo ya kara da cewa labarin da aka samu daga mambobin kungiyar yan Najeriya mazauna Malvern ya bayyana cewa an kona akalla shaguna 50 cikin dare.
A cewar wani mai idon shaida a titin Jules, ya ce matasan Zulu sun kawo harin ne a shirye kuma suka babbaka duk shagon da aka san ba na dan kasa bane.

No comments:

Post a Comment

Steps to Become a Professional Engineer

 Steps to Become a Professional Engineer  Due to the large number of errors in the definition of technical expertise, I decided to make this...