Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, saidai abin tambaya anan shi ne : menene yake kawo matsaloli tsakanin kishiya da kishiya, kuma ta yaya za'a iya warware su :
1. Jahilci : ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar : rage yawan zawarawa da 'yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi s.a.w.
2. Mummunan zato: yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima. Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba'a samu matsala ba.
3. Rashin adalci daga wajen namiji: ta yadda zai karkata zuwa ga daya daga cikin matansa, hakan sai ya sa dayar ta ce ba ta yarda ba. Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne : babu yadda za'a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi s.a.w. ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A'isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan kirdadi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne : rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum.
4. Munafukai: masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli.
No comments:
Post a Comment