Tuesday, September 3, 2019

Ahmad musa ya bayyana abinda yasa ya zama captain din super eagles

Jigon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, kuma jagoran kungiyar, Ahmad Musa ya bayyana cewa duk nasarar daya samu a harkar kwallon kafa ya sameta ne sakamakon jajircewa da aiki tukuru.
Musa ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Satumba yayin daya ziyarci sansanin FIFA Goal project dake Abuja inda yan wasan U23 na Najeriya suke atisaye kafin karawarsu da kasar Sudan don samun tsallakewa zuwa gasar U23 na nahiyar Afirka gaba daya.Musa ya yi kira ga yan wasan da suka saki jiki su yi kwallo domin yi ma kasar alfahari ta hanyar lallasa kasar Sudan a gidansu tare da hayewa zuwa gasar cin kofin nahiyar Afirka na yan wasa yan kasa da shekaru 23.
“Na zo nan ne domin na baku kwarin gwiwa tare bayyana muku goyon bayana a gareku saboda muhimmancin wannan wasa dake gabanku, na yi wasa a U23 kafin na fara buga ma Eagles a shekarar 2010, kuma sakamakon jajircewa da aiki ba kyuya tare da ikon Allah a yanzu ni ne kyaftin na Eagles.
“Allah Ya azurta Najeriya da hazikan yan wasa da dama, na zama jagoran yan wasan Super Eagles ne ba wai don na fi sauran ba, amma dai saboda jajircewa da kuma mayar da hankali a kan aiki na, don haka nake kira a gareku ku tafi Sudan ku lallasasu don mu haye zuwa gasar Olympic.” Inji shi.

No comments:

Post a Comment

Steps to Become a Professional Engineer

 Steps to Become a Professional Engineer  Due to the large number of errors in the definition of technical expertise, I decided to make this...