Tun bayan dana fitar da rubutuna da nayi mai taken "Gareku Samari masu shirin yin Aure" nake ta samun sakonni iri-iri daga wajen mata, wadanda galibinsu suna kalu-balanta ta ne akan ya kamata suma na haska musu hanyar da zasu gane miji nagari. Wata baiwar Allah mai suna Maryam El-hussain ta dan dorani a hanya, domin kuwa ta fara jero wasu halayen mazan da ba na kwarai ba. Saidai batayi dogon bayani akai ba. Ammadai na karasa mata. Ga jerin halayen:-
1-Duk Namiji dan gata ki kiyaye shi.
2- Duk Namijin da baya aiki ko sana'a ki kiyaye shi.
3-Duk Namijin da bashi da illmi addini ki kiyaye shi.
4- Duk Namijin da yake shaye ---shaye ki kiyaye shi.
5- Duk Namijin da ya nuna kwadayin abin hannunki ko na iyayenki ki kiyaye shi.
6- Duk namijin da yacika kule-kulen mata ki kiyaye shi.
7- Duk namijin da bai damu da ibada ba ki kiyaye shi.
8- Duk namijin da baya ganin girman nagaba dashi ki kiyaye shi.
HUJJAH
1- Dan gata shine wanda iyayensa suke goyon bayanshi akan duk wani abu da ya aikata mai kyau ko mara kyau. Iyayensa sun sangarta shi tun yana karami, ya taso ne baya iya ban-bance daidai da ba dai-dai ba.
2- Daga lokacin da aka daura muku aure, cinki da shanki da suturarki duk sun rataya a wuyan mijinki, kinga ko idan baya sana'a babu yadda za ai ya iya daukar dawainiyarki, saidai ma yayita kokarin rabaki da naki.
3- Neman ilimi farillah ne akan dukkan musulmi, haka nan Ilimin addini shi zai yi muku jagora a zaman aurenku, jahilci duhu ne wanda yake saurin makantarwa.
4- Dan shaye-shaye bashi da hankalin da zai iya kulawa dake, ko da ace zai iya kulawa dake tofa zabai iya kulawa da tarbiyyar 'ya'yanku ba.
5- Namijin da ya nuna yana kwadayin abin hannunki ko na iyayenki tofa ba tsakaninsa da Allah yake sanki ba, yana sanki ne dan wannan dukiyar da kike da ita, duk soyayyar da ba dan Allah ake yinta ba, to fa dole akwai ranar da zatazo karshe.
6- Zaki sha bakin ciki da takaici idan kika auri namiji mai kule-kulen mata, kai galibinsu ma auri saki garesu, domin daga sunga burwa mai kyau sai su fara tunanin yadda za ai su aureta, galibinsu ma dai auren sha'awa suke ba auren soyayya ba.
7- Rashin yin ibada na nuna rashin tsoran Allah, haka kuma wanda baya tsoron bazai taba yi miki adalci ba, sallah tana daya daga cikin rukunan musulunci guda biyar.
8- Akwai hatsari a auren wanda baya ganin girman nagaba dashi, domin hatta iyayanki ma bazai ga girmansu ba, baya ganin kowa da gashi, duk sanda kuka sami sabani dashi sai kirasa wanda zaki kaiwa kararsa.
Wadannan sune halaye guda takwas na Mazan da yakamata mata su kiyaye su. Dafatan 'Yanmata za a kiyaye.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Steps to Become a Professional Engineer
Steps to Become a Professional Engineer Due to the large number of errors in the definition of technical expertise, I decided to make this...
-
Sanin kowa ne jindadin rayuwa sai mutum ya sami irin Macen da yake so sannan zai gane a dadi yake ko a wahale. Ta yaya zaka shawo kan mace...
-
Kishi wata dabi'a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A'isha tana cewa : "Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na ...
No comments:
Post a Comment